Acts 12

Kuɓuta Mai Ban mamakin da Bitrus Ya Yi Daga Kurkuku

1Kusan a wannan lokaci ne Sarki Hiridus ya kama waɗansu da suke na ikkilisiya, da niyya ya tsananta musu. 2Ya sa aka kashe Yaƙub, ɗanʼuwan Yohanna, da takobi. 3Saʼad da ya ga wannan ya faranta wa Yahudawa rai, sai ya kama Bitrus shi ma. Wannan ya faru kwanakin Bukin Burodi Marar Yisti. 4Bayan ya kama shi, sai ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, don su yi gadinsa. Hiridus ya yi niyyar ya yi masa shariʼa a gaban mutane bayan Bikin Ƙetarewa.

5Saboda haka aka tsare Bitrus a kurkuku, amma ikkilisiya ta nace da adduʼa ga Allah dominsa.

6A daren da in gari ya waye da Hiridus yake niyyar kawo shi domin a yi masa shariʼa, Bitrus yana barci tsakanin sojoji biyu, ɗaure da sarƙoƙi biyu, masu gadi kuma suna bakin ƙofa. 7Ba zato ba tsammani sai malaʼikan Ubangiji ya bayyana haske kuma ya haskaka a ɗakin. Ya bugi Bitrus a gefe ya kuma tashe shi, ya ce, “Maza, ka tashi!” Sarƙoƙin kuwa suka zube daga hannuwansa.

8Saʼan nan malaʼikan ya ce masa, “Ka sa rigunarka da takalmanka.” Bitrus kuwa ya sa. Malaʼikan ya faɗa masa cewa, “Ka yafa mayafinka ka bi ni.” 9Bitrus ya bi shi suka fita kurkukun, amma bai ma san cewa abin da malaʼikan yake yi tabbatacce ne ba; yana tsammani wahayi yake gani. 10Suka wuce masu gadi na fari da na biyu, suka kuma isa ƙofar ƙarfe ta shiga birni. Ƙofar kuwa ta buɗe musu da kanta, suka kuma wuce. Saʼad da suka yi tafiya tsawon wani titi, nan take malaʼikan ya bar shi.

11Sai Bitrus ya dawo hankalinsa, ya ce, “Yanzu na sani ba shakka Ubangiji ne ya aiki malaʼikansa yǎ cece ni daga hannun Hiridus da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.”

12Da ya gane haka, sai ya tafi gidan Maryamu uwar Yohanna, wanda ake kuma kira Markus, inda mutane da yawa suka taru suna adduʼa. 13Bitrus ya ƙwanƙwasa ƙofar waje, sai wata mai aiki a gidan da ake kira Roda ta zo tǎ ji ko wane ne. 14Da ta gane muryar Bitrus, ta cika da murna ta gudu ta koma ba tare da ta buɗe ƙofar ba, sai ta koma a guje ta ce da ƙarfi, “Ga Bitrus a bakin ƙofa!”

15Sai suka ce mata, “Kina hauka.” Da ta nace cewa shi ne, sai suka ce, “To, lalle, malaʼikansa ne.”

16Amma Bitrus ya yi ta ƙwanƙwasawa. Da suka buɗe ƙofar suka kuma gan shi, sai suka yi mamaki. 17Bitrus ya yi musu alama da hannunsa su yi shiru sai ya bayyana yadda Ubangiji ya fitar da shi daga kurkuku. Ya ce, “Ku gaya wa Yaƙub da kuma ʼyanʼuwa game da wannan,” saʼan nan ya tashi ya tafi wani wuri.

18Da safe, hargitsin da ya tashi tsakanin sojojin ba ƙarami ba ne, a kan abin da ya sami Bitrus. 19Bayan Hiridus ya neme shi bai same shi ba, sai ya tuhumi masu gadin, ya kuma ba da umarni a kashe su.

Mutuwar Hiridus

Saʼan nan Hiridus ya tashi daga Yahudiya ya tafi Kaisariya ya kuma yi ʼyan kwanaki a can.
20Yana da rashin jituwa da mutanen Taya da na Sidon; sai suka haɗa kai suka nemi ganawa da shi. Bayan suka sami goyon bayan Bilastus, amintaccen bawan sarki, sai suka nemi salama, domin sun dogara ga ƙasar sarkin don samun abincinsu.

21A ranar da aka shirya Hiridus, sanye da kayan sarautarsa, ya zauna a gadon sarautarsa ya kuma ya wa mutanen jawabi. 22Suka ta da murya suka ce, “Wannan muryar wani allah ne, ba ta mutum ba.” 23Nan take, domin Hirudus bai yi wa Allah yabo ba, wani malaʼikan Ubangiji ya buge shi, tsutsotsi kuwa suka cinye shi ya kuma mutu.

24Amma maganar Allah ta ci gaba da ƙaruwa ta kuma bazu.

25Saʼad da Barnabas da Shawul suka kammala aikinsu, sai suka komo daga Urushalima, tare da Yohanna, wanda ake kira Markus.

Copyright information for HauSRK